Faransa

Macron ya bukaci tsagaita wuta mai dorewa a Syria

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Francois Mori/Pool via REUTERS

A wata ganawa da suka yi a fadar Elysee, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga kasashen Turkiya da Rasha da su a aiwatar da tsarin tsagaita wuta mai dorewa a yankin Idlib na kasar Syria

Talla

Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata dakarun gwamnatin Syria da ke samun goyon bayan Rasha suka shiga dirar mikiya kan tungar karshe ta ‘yan tawaye da ke samu tallafin Turkiyya.

Macron ya bayyana takaicinsa ga shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da na Rasha Vladimir Putin kan matsalar jinkai da ke ci gaba da wanzuwa a yankin da rikici ya daidaita.

Macron ya yi kashedin cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda na iya yaduwa duba da irin matakan soji da gwamnatin Syria da abokan ta ke dauka, yana mai cewa ya saba wa yarjejeiyar da aka cimma tsakanin Rasha da Turkiyya a Idlib a shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI