Abokan hamayya sun goyi bayan Biden a zaben fidda gwani

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrats Joe Biden.
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrats Joe Biden. Alex Wong/Getty

Yau 'yan Jam’iyyar Democrat a Amurka ke gudanar da zaben fidda gwani a Jihohi 14 da akewa lakabi da ‘Super Tuesday’ domin zabo wanda zai fafata da shugaba Donald Trump a zaben kasa baki daya da zai gudana a watan Nuwamba.

Talla

Tuni 3 daga cikin masu neman tikikin Jam’iyyar suka janye inda suka bayyana goyan bayan su ga tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, cikin su harda Pete Buttigieg da Sanata Amy Kloubachar da Beto O’Rourke.

Yanzu haka mutane 5 suka rage amma masu sa ido na kallon Sanata Bernie Sanders da Joe Biden a matsayin wadanda zasu kai matakin karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.