Coronavirus

Fargabar Coronavirus ta ta'azzara a Amurka

Irin jirgin ruwan yawon bude ido da dubban mutane suka makale a California saboda fargabar cutar Coronavirus.
Irin jirgin ruwan yawon bude ido da dubban mutane suka makale a California saboda fargabar cutar Coronavirus. AFP

Dubban mutane, makale a wani jirgin ruwa na yawon bude ido a Carlifornia ne suka rasa na yi, sakamakon fargabar cutar Coronavirus, bayan an samu fasinjoji da ma’aikatan jirgin da alamun cutar, a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ke cewa lamarin ya janyo tsaiko a bangaren sufuri da jigilar kayayyakin masarufi a fadin kasar, yayin da sauran kasashen duniya ke neman mafita.

Talla

Jami’ai sun jinkirta dawowar jirgin ruwan, mai suna Grand Princess birnin San Francisco daga Hawaii a daren Laraba don yin gwajin tantance wadanda ake ganin sun harbu da cutar.

Wani mutum mai shekaru 71 da ya yi balaguro zuwa Mexico ta cikin jirgin ya mutu bayan harbuwa da cutar ta COVID 19, mjutum na farko kenan a California, kamar yadda gwamnan jihar Gavin Newsom ya sanar.

Wata sanarwa da kamfanin sufurin jiragen ruwa na Princess Cruises ya aike wa kamfanin dillancin labaran Faransa ta ce kimanin mutane 62 daga cikin fasinjojin jirgin ruwan dubu 2 da dari 5 ne aka killace har sai an tantance matsayinsu game da cutar.

A wani mataki mafi tsauri da wata kasar Turai ta dauka tun da wannan cuta ta kuno kai kuwa, Italiya ta sanar da rufe illahirin makarantun kasar, kanana da manya har zuwa ranar 15 ga wannan wata bayan cutar ta kashe mutane 107.

A bangaren sufurin jiragen sama kuwa, cutar COVID 19 ta janyo kamfanin Lufthansa ya dakatar da jiragensa 150 daga tashi, yayin da a Alhamis dinnan, kamfanin Flybe mafi girma a Birtaniya, mai daukar fasinjoji miliyan 8 a shekara, ya dakatar da dukkannin jiragensa daga zirga zirga

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.