Za a rufe majami'ar Bethlehem saboda annobar corona

Cikin majami'ar Bethlehem
Cikin majami'ar Bethlehem AFP/Thomas Coex

Za a rufe majami’ar nan da aka gina a Bethlehem, wajen da aka yi amannar cewa mahaifar Annabi Isa Alaihilsalam ne, sakamakon fargabar shigowar coronavirus a wani otel a yankin yamma da kogin Jordan, inda Isra’ila ta mamaye.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ta ce majami’ar ta kasance a bude ya zuwa safiyar Alhamis dinnan, amma wani jami’in cocin da bai so a bayyana sunansa ba ya ce sunaa girmama gwamnati, kuma za su yi biyayya saboda rigakafi ya fi magani.

Tun da farko, hukumomi a ma’aikatar lafiya ta yankin Falasdinu sun sanar cewa ana tunanin akwai wadanda ke dauke da wannan cuta ta coronavirus a wani otel a yankin Bethlehem,karon farko yankin Falasdinawa.

Shugaban ma’aikatar lafiyar, Imad Shahadeh, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewav wasu masu yawon bude ido dag Girka sun ziyarci otel din a karshen watan Fabrairu, kuma daga baya an gano biyu daga cikinsu na dauke da cutar.

An gano mutane 4 daga cikin ma’aikatan otel din da ake fargabar sun harbu da cutar ta coronavirus, kuma ana sa ran za a tabbatar da sun harbu din bayaan gwaji a Alhamis dinnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI