Girka-Turkiya

An yi arrangama tsakanin 'yan sandan Girka da 'yan gudun hijira

Wasu daga cikin gungun 'yan gudun hijirar da suka yi arrangama da 'yan sandan kasar Girka akan iyaka da Turkiya.
Wasu daga cikin gungun 'yan gudun hijirar da suka yi arrangama da 'yan sandan kasar Girka akan iyaka da Turkiya. AFP/BULENT KILIC

An yi wata kazamar arrangama tsakanin ‘yan gudun hijira da ‘yan sandan Girka akan iyakar kasar da Turkiya, a lokacin da dubbansu suka yi yunkurin shiga kasar ta Girka don isa cikin nahiyar Turai.

Talla

Dubban ‘yan gudun hijirar ne dai ke ci gaba da rankayawa kan iyakar Girka, bayan da makon jiya shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya sanar da kawo karshen yarjejeniyar 2016 tsakaninsa da kasashen Turai, ta taimaka musu wajen hana bakin-haure kwarara zuwa nahiyar, indaza su rika bada miliyoyin euro domin kula da ‘yan gudun hijirar a Turkiya.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Turkiya da kasashen Turai sakamakon rashin amsa bukatar shugaba Erdogan na dakatare da hare-haren sojin Syria a lardin Idlib mai iyaka da Turkiya, lamarin da ya kai ga halaka sojojinta akalla 35.

A baya bayan nan ne dai kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da shinta na ware karin Euro miliyan 500 a matsayin tallafi ga ‘yan gudun hijirar Syria da ke rayuwa a Turkiya.

Kungiyar ta EU za ta bada tallafin ne domin sassauta tankiyar da ta kunno kai tsakaninta da Turkiya a baya bayan kan hare-haren da sojin Syria ke kaiwa ‘yan tawaye a lardin Idlib, da yayi iyaka da ita, inda dakarun na Syria suka halaka mata sojoji akalla 35.

Tallafin makuden kudaden na zuwa ne bayan hukumomin Kungiyar Tarayyar Turai sun caccaki Turkiya da yi masu zagon-kasa ta hanyar bude kan iyakarta da Girka don bai wa dubban ‘yan gudun hijirar Syria kwarara cikin nahiyar Turan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI