Turai-Turkiya

Turkiya ta hana 'yan ci rani ketara tekun Aegean

Wasu bakin-haure da 'yan ci rani, bayan isa tsibirin Lesbos na kasar Girka. 2/3/2020.
Wasu bakin-haure da 'yan ci rani, bayan isa tsibirin Lesbos na kasar Girka. 2/3/2020. AFP

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya baiwa jami’an tsaron gabar ruwan kasar umarnin hana ‘yan ci rani tsallaka mashigin tekun Aegean don isa nahiyar Turai, da zummar kaucewa arranagamar da ake yi tsakanin bakin-hauren da jami’an tsaron Girka, akan iyakar kasar da Turkiya dake kan tudu.

Talla

Dubban bakin-haure ne dai daga Turkiyan suka kwarara zuwa iyakar Girka da aniyar shiga Turai, bayan da shugaba Erdogan ya sha alwashin daina hanasu kwarara zuwa Turan, matakin da ya kara tsamin dangantaka tsakanin kasashen Turan da Turkiya.

Turkiya dai na fatan matsain lamba ga kasashen na Turai domin tsawatarwa Syria daina kai hare-hare a lardin Idlib inda ta halaka sojin Turkiya akalla 35, yayinda Turan ke zargin Turkiyan da yin amfani da ‘yan gudun hijirar a matsayin makamin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI