Za a cigaba da gangamin siyasa duk da bullar Coronavirus - Trump
Shugaban Amurka Donald Trump, yace bashi da niyyar dakatar da taruka ko gangamin siyasa, duk da karuwar wadanda annobar murar Coronavirus ke shafa a kasar.
Wallafawa ranar:
Shugaban na Amurka ya shaidawa manema labarai matsayin nasa ne, a dai dai lokacin da adadin wadanda suka kamu da cutar ta Coronavirus a Amurka ya zarta 400, wasu 19 kuma suka mutu a dalilin annobar, mafi akasari a yammacin birnin Washington.
Zuwa wannan lokaci dai hukumomin lafiya sun ce wannan anoba ta halaka mutane sama da dubu 3 da 500, gami da shafar wasu sama da dubu 100 a fadin duniya, sai dai mafi rinjaye wadanda annobar ta rutsa da su na a kasar China, makyankyasar cutar.
A yanzu haka dai kasashen da annobar ta fi muni cikinsu bayaga China sun hada da Korea ta Kudu, inda annobar ta halaka sama da mutane 42 wasu dubu 6 da 234 suka kamu, sai Italiya inda cutar ta kama mutane dubu 4 da 636 ta kuma halaka wasu 197, sai Iran da annobar ta halakawa mutane 145, wasu dubu 4 da 747 kuma suka kamu. A Faransa kuwa annobar ta Corona ta kashe mutane 16 kawo yanzu, wasu 949 kuma sun kamu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu