Faransa

Macron na fuskantar kalubale a zaben Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Gonzalo Fuentes

Shekaru 3 bayan samun gagarumar nasarar lashe zaben shugaban Faransa da aka yi a shekarar 2017, shugaba Emmanuel Macron na fuskantar kalubalae sosai a zabukan da za a fara na mazabu daga karshen wannan mako.

Talla

Wannan zabe zagaye na farko da zai gudana a karshen wannan mako zai zama zakaran gwajin dafi kan farin jinin shugaba Emmanuel Macron da kuma magoya bayansa, bayan zanga-zangar adawa da manufarsa da aka dauki dogon lokaci ana yi a Faransa.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewar, jam’iyyar shugaba Macron ta LREM za ta fuskanci matsaloli a zaben na wannan mako, kafin wanda zai gudana ranar 22 ga wannan wata saboda yadda gwamnatin ta yi gaban kanta wajen amincewa da dokar fansho da ake adawa da ita.

Shugaba Macron wanda ake sa ran ya tsaya takarar neman wa’adi na biyu a shekarar 2022, ya ki amincewa cewa, jam’iyyarsa na fuskantar kalubale a wannan zabe mai  zuwa wanda za a zabi kansiloli sama da 500,000 da Magadan Gari kusan 35,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI