Coronavirus ta kashe fiye da mutane 500 a Turai
Wallafawa ranar:
Adadin mutanen da cutar coronavirus ta kashe a nahiyar Turai ya zarce 500 yanzu haka, sakamakon karuwar mamatan da aka samu a kasar Italiya, kasar da cutar tafi illatawa a nahiyar baki daya.
Hukumar kula da kare lafiyar jama’a tace a jiya litinin mutane 97 suka mutu, abinda ya kawo adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa 463, abinda ya sa gwamnatin kasar daukar matakai masu tsauri ciki harda killace mutane sama da miliyan 16 a cikin gidajen su.
Ya zuwa yammcin jiya kasar Italia kawai ta samu rabina dadin mutane 854 da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar a wajen China.
Alkaluma sun nuna cewar mutane 511 suka mutu da cutar a Turai, wadanda suka hada da 21 a Faransa 16 a Spain, 4 a Birtaniya sai kuma 3 a Netherlands, 2 a kasashen Switzerland da Jamus, yayin da adadin mutanen da cutar ta kama a Yankin ya kai 9,172, wanda ya nuna karuwar 1,797 daga alkaluman da aka bayar ranar lahadi.
Hukumomin lafiyar Italia sun ce mutane 733 yanzu haka suna kwance a gobe da nisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu