Amurka

Amurka na nazarin hana baki daga Turai zuwa kasar

Kasar Amurka na nazarin domin daukar matakin hana baki daga kasashen Turai zuwa kasar ta saboda yadda cutar coronavirus ta yadu a nahiyar.

Likitocin da ke kula da masu fama da cutar coronavirus.
Likitocin da ke kula da masu fama da cutar coronavirus. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Mukaddashin Sakataren cikin gida Ken Cuccinelli yace batun mai girma ne kan yadda Amurka zata yi da Turai baki daya, kuma yanzu haka suna Nazari akai.

Cuccinelli ya shaidawa kwamitin Majalisar wakilai cewar halin da ake ciki a Turai abin fargaba ne, musamman yankin Schengen da kofar shigar sa ke bude ga baki daga Yammacin Turai.

Ita ma kasar Amurka na fama da wannan cuta wadda tuni mutane sama da 30, bayan ta kama mutane akalla 1,000

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI