EU ta ware Euro biliyan 25 don magance coronavirus

Shugabannin Majalisar Turai
Shugabannin Majalisar Turai Kenzo Tribouillard/Pool via REUTERS

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun gudanar da taron gaggawa ta hanyar tattaunawa da fasar hoton bidiyo a jiya Talata, yayin da suke kokarin daukan matakin bai daya dangane da cutar coronavirus, wadda ta haifar da cikas ga kasuwanni tare da tsunduma Italiya cikin wani yanayi.

Talla

A yayin da wasu kasashen Asiya suke baiyana fatan samun saukin annobar cutar coronavirus, ta wajen cin karfin yaduwarta, cutar ta ci gaba da zama barazana ga kasashen Turai, masamman a Italiya kasar da cutar ta fi muni a wajen kasar China inda ta samo asali.

Coronavirus ta kashe sama da mutane 450 a Italiya cikin sama da dubu 9 da suka kamu da ita, lamarin da ya tilastawa kasar daukar tsauraran matakai don sassauta yaduwar cutar.

Gabanin wannan taro ta hanyar fasahar zamani ta bidiyo da shugabannin Turai 27 suka gudanar, sai da Hukumar zartarwar Turai ta yaba wa kasar Italiya saboda kwararan matakan da ta dauka don yakar cutar COVID-19, wadanda suka hada da umurtan al’ummar kasarta miliyan 60 da su kasance a gidajensu, batare da fita ba, sai a yanayi na bukatar gaggawa.

Taron tattaunawar gaggawa ta hoton bidiyo, an yi shi ne, domin amincewa da daukar matakin baidaya tsakanin kasashe mambobin kungiyar kan yakar cutar coronavirus, a dai-dai lokacin kananan kasashen ke zargin Faransa da Jamus da tafiya su kadai, ta hanyar haramta fitar da wasu magungunan kasashensu.

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar kasar ta fara shiga cikin halin tsaka mai wuya sakamakon barkewar cutar coronavirus wadda ta kashe mutane 33 bayan kama mutane 1,784.

Bayan ziyarar da ya kai hukumar gudanar da motocin daukar marasa lafiya, shugaban ya nemi kwantar da hankalin al’ummar kasar, inda yace suna iya bakin kokarin su wajen shawo kan matsalar.

Cikin wadanda suka kamu da cutar a Faransa harda ministan al’adu da Yan Majalisu guda 5 da kuma wasu jami’an gwamnati.

Shugaba Macron yayi wannan jawabin ne bayan taron tattaunawar bidiyo da ya yi da sauran takwarorin sa na Turai, inda ya yi karin bayani kan irin matakan da suke dauka.

Kuna iya latsa alamar sauti dake kasa don sauraran abin da yake cewa.

EU ta ware Euro miliyan 5 don magance coronavirus

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.