Tsakanin mutane dubu 5 zuwa 10 ne coronavirus ta kama a Birtaniya
Gwamnatin Birtaniya ta ce akalla mutane tsakanin 5,000 uwa 10,000 na dauke da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 a cikin kasar, kuma wasu daga cikin su basu sani ba.
Wallafawa ranar:
Babban masanin kimiyar dake baiwa gwamnati shawara Patrick Vallance ya bayyana haka inda ya ce ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutane 590 da suka kamu da ita, yayin da wasu da dama basu yi gwajin da zai tabbatar musu samun cutar ba.
Firaminista Boris Johnson ya tabbatar da mutuwar mutane 10, yayin da ya ce suna daukar matakan da suka dace wajen shawo kan cutar.
Johnson ya bukaci mutane su yi ta wanke hannayen su, kuma su dinga neman taimakon likita da zaran sun fara ganin alamun cutar.
Firaministan wanda yace ba zasu rufe makarantu ba har sai idan hakan ya zama dole, yace zasu dinga sauraron shawarwarin masana harkar kula da lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu