Faransa

Masu rigunan dorawa sun bijirewa fargabar annobar Corona

Wasu daga cikin daruruwan Faransawa masu adawada gwamnatin Emmanuel Macron.
Wasu daga cikin daruruwan Faransawa masu adawada gwamnatin Emmanuel Macron. Reuters

Daruruwan Faransawa masu sanya da rigunan dorawa dake adawa da gwamnati, sun bijirewa gargadin haramta tarukan da ya kunshi sama da mutane 100 a kasar saboda annobar murar Coronavirus.

Talla

Yau asabar dai daruruwan masu rigunan dorawar sun yi dandazo a birnin Paris yayin zanga-zangar ta kin jinin gwamnati karo na 70 da suka saba yi duk mako tun daga watan Nuwamban shekarar 2018.

A wani labarin kuma a karon farko an samu wani fursuna da ya kamu da cutar murar ta coronavirus a kasar ta Faransa, yayinda kuma a karon farkon shima wani dan majalisar dattijan kasar ya kamu.

Dangena da zabukan dake shirin yi kuma, gwamnatin Faransa ta ce zaben kananan hukumominta zai gudana kamar yadda aka tsara a gobe lahadi 15 ga maris, duk da fargaba kan annobar murar Coronavirus da bulla a kasar.

Yayin sanar da matakin gudanar zaben, gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta bayyana daukar dukkanin matakan kare jama’a daga yaduwar annobar.

Kashin farko na zaben magadan garin zai gudana ne a ranar lahadi, yayinda kuma za a yi zagaye na 2 a makon gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI