Faransa

Za a gurfanar da masu hannu a harin birnin Paris

Wasu daga cikin jami'an tsaron Faransa
Wasu daga cikin jami'an tsaron Faransa REUTERS/Benoit Tessier

Manyan alkalan Faransa sun umarci gurfanar da mutane 20 da ake zargi da hannu a harin shekarar 2015 a birnin Paris da ya yi sanadiyar kashe mutane 130.

Talla

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Faransa suka kammala gudanar da bincike a kan munanan hare-haren da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.

Sai dai kawo yanzu ba a sanar da ranar yin shari’ar wadda ke kunshe da masu shigar da kara dubu 1 da dari 765 kuma da dama daga cikinsu 'yan-uwa ne ga mutanen da suka gamu da ajalinsu a hare-haren.

A kalla mutane 130 suka gamu da ajalinsu a ranar 15 ga watan Nuwamban 2015 sakamakon munanan hare-haren da wasu 'yan bindiga 10 suka kai a filin wasan kwallo da ke wajen birnin Paris da gidan rawa na Bataclan da ma wuraren cin abinci.

Kodayake jami’an 'yan sandan kasar sun yi nasarar kashe maharan bayan da suka tada bama-baman da ke dauke da su illa Saleh Abdeslam, wanda watanni 4 bayan aukuwar lamarin ya shiga hannun jami’an.

Ko a watan Nuwamban shekarar bara, masu hukunta manyan laifuka a Faransa sun tuhumi mutane 14 wadanda kawo yanzu ke tsare a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.