China-Amurka

Takaddama ta barke tsakanin Amurka da China kan Coronavirus

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst

Kasashen Amurka da China sun fada cikin cacar baka dangane da zargin cewar Amurka ce ta samar da cutar coronavirus domin hallaka jama’ar ta.

Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci China ta daina daukar matakan bata mata suna dangane da wannan zargi, a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ke bayyana cutar a matsayin ta kasar China.

Sakon da ya aike ta kafar twitter inda ya bayyana cutar a matsayin cutar China ya harzuka gwamnatin kasar wadda ta nuna rashin jin dadin ta.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Zhao Lijian a makon jiya yacce suna kyautata zaton cutar ta samo asali ne daga Amurka amma ba Wuhan ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace Pompeo ya tattauna da Yang Jiechi, babban jami’in harkokin wajen China inda ya nuna masa bacin ran kasar dangane da zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI