Muhawara ta kaure kan makomar gasar Premier ta Ingila
Wallafawa ranar:
Tsohon dan wasan Arsenal Paul Merson ya caccaki shawarar da wasu ke bayarwa kan makomar gasar Premier Ingila, wadanda ke ganin kamata yayi a baiwa kungiyar Liverpool kofin gasar ta bana, bayanda annobar coronavirus ta tilasta dakatar da gasar.
A halin da ake ciki matakin farko, hukumar kwallon kafar ingila ta dakatar da gasar Premier ce zuwa ranar 4 ga Afrilun dake tafe, da fatan za a shawo kan annobar zuwa lokacin, wanda muddin aka samu akasin haka to sai kuma abinda hali yayi.
Bayan fafata wasanni 29 daga cikin 38 na gasar ta Premier, Liverpool ke kan gaba da maki 82, tazarar maki 25 tsakaninta da ta biyu Manchester City mai maki 52.
Karin maki 6 ko samun nasara a wasanni 2 ya ragewa Liverpool din ta zama zakarar gasar ta bana, abinda yasa wasu ke da ra’ayin kamata yayi kawai “a bada kai bori ya hau” wato a mikawa kungiyar ta Liverpool.
Rabon da Liverpool ta lashe kofin gasar Premier tun shekaru 30 da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu