Coronavirus

Bankin Turai ya ware euro biliyan 750 don rage radadin annoba

Shugabar babban bankin nahiyar Turai Christine Lagarde.
Shugabar babban bankin nahiyar Turai Christine Lagarde. REUTERS/Kai Pfaffenbach

Babban Bankin kasashen Turai ya kaddamar da shirin gaggawa da ya kunshi euro biliyan 750 domin rage radadin matsalar da cutar coronavirus ta yiwa tattalin arzikin kasashen dake Yankin.

Talla

A karkashin shirin Bankin zai saye bashin da gwamnatocin Yankin da kamfuna ke da shi, cikin su harda da na kasashen Girka da Italia dake fama da matsalar tattalin arziki domin taimaka musu ficewa daga wannan matsala.

Shugabar Bankin Christine Lagarde tace babu wani shinge da suka saka dangane da wannan yunkurin na su na kare darajar kudin euro.

A makwannin da suka gabata gwamnatocin kasashe daban daban sun bayyana irin matakan da suka dauka na taimakawa kamfanoni da masana’antun kasashen su sakamakon wannan matsala dake neman durkusar da tattalin arzikin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.