Amurka za ta yi amfani da Chloroquine don magance Coronavirus
Shugaban Amurka Donald Trump yace gwamnatinsa za ta yi amfani da maganin zazzabin cizon sauro da akafi sani da Chloroquine wajen yaki da cutar coronavirus wadda yanzu haka ta kashe mutane 150 a fadin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Trump ya bayyana cewar za su gaggauta samar da maganin wanda aka tabbatar da ingancinsa domin yakar cutar.
Yayin sanar da matakin shugaba Trump ya ce abin farin ciki shi ne yadda aka dade ana amfani da maganin, saboda haka akwai kwarin gwiwar cewa idan maganin baiyi nasara ba, ba zai kashe kowa ba, sabanin sabon maganin da ba a iya sanin abinda zai biyo bayan shansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu