Faransa

Coronavirus ta halaka karin Faransawa 78 a kwana 1

Ma’aikatar Faransa ta ce cutar murar Coronavirus ta halaka karin mutane 78 a kasar a kwana guda, abinda ya sanya jimillar wadanda annobar ta halaka tun bayan bulla a kasar kaiwa 450.

Wasu makota a birnin Paris, yayin zantawa da juna daga nesa. 20/3/2020.
Wasu makota a birnin Paris, yayin zantawa da juna daga nesa. 20/3/2020. Martin BUREAU / AFP/ MANILA BULLETIN
Talla

Yanzu haka kuma mutane dubu 12 da 612 aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasar.

A larabar da ta gabata Faransa ta fuskanci adadi mafi muni na mutanen da suka mutu a dalilin annobar, bayan salwantar rayuka 108 a kwana daya.

Alkalumman jami'an lafiyar Faransa a baya bayan nan sun nuna cewar adadin wadanda suka kamu da cutar murar ya zarta dubu 10, abinda ya sanya magadan garin biranen Paris da Nice, daukar matakin rufe filayen shakatawa, da sauran wuraren taruwar jama'a da suka rage a bude, domin dakile cigaba da yaduwar annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI