Faransa za tayi amfani da jiragen sama wajen hana mutane fita

Gwamnatin gwamnatin Faransa ta ce za ta yi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu da kuma jiragen sama masu sarrafa kan su wajen hana mutane fita daga gidajen su saboda yaduwar cutar coronavirus bayan an samu karin mutane 108 da suka sake mutuwa yau Asabar.

Ma'aikatan jinya dauke da micutar coronavirus a gabashin Faransa.
Ma'aikatan jinya dauke da micutar coronavirus a gabashin Faransa. AFP
Talla

Ma’aikatar tsaron Jandarmomi ta sanar da cewar jiragen saman zasu taimaka wajen gano masu karya dokar da aka saka domin hukunta su.

Ko a yau an gwada amfani da jirgin guda a birnin Paris inda ya dinga shawagi daga unguwa zuwa unguwa domin sanya ido,  yayin da za’ayi amfani da jiragen sama masu sarrafa kan su wajen sanya ido a gabar ruwan kasar.

Ya zuwa yanzu mutane 372 suka mutu sakamakon karin mutane 108 da aka samu yau Asabar, yayin da mutane sama da 9,000 suka kamu da cutar.

Gwamnatin ta kuma sanya tarar euro 135 akan duk wanda ya bar gidan sa ba tare da izini ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI