Kasashen Latin sun dukufa kan matakan dakile annobar Coronavirus

Mutane na cigaba da zirga-zirga a yankin Ladeira Porto Geral, dake birnin Sao Paulo a Brazil duk da barazanar Coronavirus da ta bulla a kasar. 16/3/2020.
Mutane na cigaba da zirga-zirga a yankin Ladeira Porto Geral, dake birnin Sao Paulo a Brazil duk da barazanar Coronavirus da ta bulla a kasar. 16/3/2020. Reuters

Shugaban Colombia Ivan Duque daga ranar talata 24 ga watan da muke ciki, zuwa 13 ga watan Afrilu, za a haramtawa daukacin ‘yan kasar zirga-zirga, domin dakile yaduwar annobar murar Coronavirus.

Talla

Jawabin shugaban na Colombia na zuwa yayinda rahotanni suka ce tuni kusan rabin al’ummar kasar suka soma killace kansu daga jiya Juma’a zuwa ranar litinin, domin gwada tasirin matakin.

Su ma kasashen Cuba da Bolivia sun ce ranar talatar dake tafe 24 ga maris za su rufe iyakokinsu saboda annobar ta Coronavirus, wadda kawo yanzu ta halaka jimillar mutane 30 a kasashen Latin, gami da shafar wasu dubu 3.

Wasu daga cikin karin kasashen na Latin da annobar murar ta bulla cikinsu kuma akwai Honduras, Brazil, Paraguay, Costarica, Guatemala, Colombia da kuma Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI