Coronavirus

Manyan biranen Amurka sun haramta zirga-zirga

Hukumomin manyan biranen Amurka da suka hada da New York da kuma Illinois, sun bi sawun California wajen haramta shiga ko fita daga cikinsu domin dakile annobar Coronavirus dake yaduwa.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis
Talla

Karin biranen Amurkan da suka haramta shige da ficen sun hada da Los Angeles da kuma Chicago.

Matakin biranen dai ya zo ne a dai dai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke ikirarin samun nasara a yakin da suke yi da annobar, duk da karuwar wadanda take kashewa da kuma shafa a kasar.

Ranar alhamis shugaban Amurka Donald Trump yace gwamnatinsa za ta yi amfani da maganin zazzabin cizon sauro da akafi sani da Chloroquine wajen yaki da cutar coronavirus wadda yanzu haka ta kashe mutane 150 a fadin kasar.

Sai dai har aynzu hukumar lafiya ta duniya WHO ba ta bayyana amincewa da shawar soma amfani maganin na Chloroquine ba a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI