Adadin wadanda cutar coronavirus ta kashe a Faransa ya kai 674

Hukumomin Faransa sun ce mutane 112 ne suka mutu a cikin sa’oi 24 sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, abinda ya kawo adadin wadanda suka mutu a kasar zuwa 674.

Ma'aikatan Lafiya na daukan wanda cutar coronavirus ta kama a gabashin Faransa.
Ma'aikatan Lafiya na daukan wanda cutar coronavirus ta kama a gabashin Faransa. AFP
Talla

Jerome Salome, jami’in kula da lafiyar kasar yace adadin wadanda suka mutu yau yayi kama da na jiya, yayin da gwamnati ke ta kokarin shawo kan cutar.

Salome yace mutane 16,018 suka kamu da cutar a fadin kasar, inda yake gargadin cewar adadin na iya zarce haka domin akwai mutanen da ba’a gwada su ba.

Yanzu haka akwai mutane 7,240 dake kwance a asibiti dauke da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI