Coronavirus ta kashe mutane fiye da 100 cikin sa'o'i 24 a Amurka

Jami'ar Johns Hopkins dake Amurka ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a kasar ya zarce 100 a cikin sa’oi 24, abin da ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 389.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis
Talla

Alkaluman da Jami’ar ta gabatar sun bayyana cewar 114 suka mutu a New York, 94 a Washington sai kuma 28 a California, yayin da cutar ta kama mutane akalla 30,000 a fadin kasar.

Gwamnatin kasar da Majalisar Dokoki na tattaunawar samar da Dala triliyan 4 nan da ranar Litinin domin tallafawa kamfanonin da annobar ta shafi ayyukan su.

Amurka, kamar sauran kasashe masu fama da cutar coronavirus ta samu tata gibin da cutar ta haifar kamar rufe masana’antu da makarantu, lamarin da ala dole ya tilasta killace miliyoyin mutane a gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI