Faransa

Coronavirus ta lakume rayuka sama da 110 cikin kwana 1

Jami'an lafiyar Faransa yayin kokarin daukar mara lafiya zuwa asibiti. 20/3/2020.
Jami'an lafiyar Faransa yayin kokarin daukar mara lafiya zuwa asibiti. 20/3/2020. REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

Ma'aikatar lafiyar Faransa ta ce a ranar asabar kadai mutane 112 cutar murar Coronavirus da ta zamewa duniya alakakai ta halaka a kasar.

Talla

A jimilace alkalumman sun nuna cewa annobar at kashe mutane 562 kenan tun bayan bullarta a kasar, yayinda wasu dubu 14 da 459 suka kamu.

Karuwar adadin rayukan da annobar murar ke lakumewa a Faransa na zuwa ne bayanda aka shiga rana ta 5 da killace miliyoyin mutane, gami da girke jami’an tsaro a sassan kasar da suka hada da yan sanda da kuma Jandarmomi dubu 100 domin tabbatar da dokar haramta zirga-zirga, ba bisa bukata ta musamman ba, da ta kunshi sayen abinci da magani.

A lahadin nan ministan Lafiyar kasar ta Faransa Olivier Vèran ya sanar da umarnin gwamnatin kasar na samar da takunkuman rufe hanci miliyan 250, da za a rabawa ‘yan kasar domin dakile yaduwar annobar Coronavirus dake cigaba da lakume daruruwan rayuka cikin kwana guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.