Croatia

Girgizar kasa mai karfi ta rikita babban birnin Croatia

Wata girgizar kasa mai karfi da aka yi a Croatia ta girgiza illahirin baban birnin kasar Zagreb, inda ta lalata dimbim gine gine ta kuma ji wa wani matashi mummunan rauni a yau Lahadi, yayin da hukumomin kasar ke yi wa al’umma kashedi da kada su tattaru a waje daya saboda yaduwar cutar coronavirus.

Birnin Elazig na gabashin Turkiyya ta fuskanci girgizar kasa a watan Janairu.
Birnin Elazig na gabashin Turkiyya ta fuskanci girgizar kasa a watan Janairu. IHA via AP
Talla

Firaministan kasar Minister Andrej Plenkovic, ya ce girgizar kasar, wacce ita ce mafi karfi tun bayan shekaru 140 ta auku ne da karfe 6 na safiyar yau Lahadi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da kasar ke kokarin yaki da annobar coronavirus, wacce ta kama mutane fiye da 200 a kasar.

Tasirin wannan girgizar kasa ta shafi ginin wata mahimmiyr majami’a a tsakiyar birnin Zagreb, kana ta lalata motocin da aka a harbr ginin.

A cikin halin rikicewa da aka shiga a yankin ne aka bad rahoton cewa wani matashi mai shekaru 15 ya gamu da ajalinsa, amma daga baya shugaban asibitin birnin Zagreb ya ce mace ce matashiya, kuma bata mutu ba, sai di tana ciki mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI