Jiragen kasa za su fara jigilar jami'an lafiya kyauta a Faransa
Kamfanin sufurin jiragen kasa na Faransa, ya ce daga yanzu, zai rika jigilar jami’an kiwon lafiya a matsayin kyauta don ba su damar isa wuraren ayyukansu, wannan kuwa a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da yaki da Coronavirus.
Wallafawa ranar:
Manyan likitoci da kanana sun yi karanci a cikin cibiyoyin kiwon lafiya da ke birnin Paris da ma sauran sassa na Faransa, a daidai lokacin da adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan cuta ya doshi 700.
Shugaban sashen jigilar fasinja na kamfanin jiragen kasa SNCF Alain Krakovitch ya ce duk jami’in kiwon lafiyar da ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa zai je wurin don taimaka wa a yakin wannan cuta, to ko shakka babu za a yi jigilarsa a matsayin kyauta.
Hakazalika, wasu jihohi a kasar ta Faransa, sun amince kananan jiragen kasa da motocin bas mallakinsu don jigilar jami’an kiwon lafiya a matsayin kyauta.
Yanzu haka dai cibiyoyin kiwon lafiya sun cika makir da marasa lafiya a kasar ta Faransa, a daidai lokacin da ake fuskantan karancin jami’an kiwon lafiya sakamakon matakin takaita zirga-zirga da mahukunta suka yi, yayin da a wasu sassan kasar aka fama amfani da sojoji don taimakawa marasa lafiya da kuma isar da su a cikin asibitoci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu