Likitan shugabar Jamus ya kamu da Coronavirus
Wallafawa ranar:
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta killace kanta bayan kamuwar likitanta da cutar Coronavirus, a dai dai lokacin da kasar ke tsaurara dokokin takaita taron jama’a a matsayin matakin kariya daga annobar.
Rahoton cewar Merkel ta yi mu’ammala da wanda ya harbu da cutar ya fito ne jim kadan bayan ta sanar da haramci kan taron mutane fiye da mutane biyu a kokarin da kasar take na dakile yaduwar cutar.
A wanan Litinin aka shirya Merkel za ta jagoranci wani zama na majalisar zartaswar kasar don amincewa da fitar da euro biliyan 822 a kokarin gwamnatinta na tallafa wa tattalin arzikin kasar sakamakon tasirin annobar ta Coronavirus.
A baya bayan nan ne dai likitan shugabar gwamnatin ta Jamus da ya kamu da cutar ya ziyarci Merkel don yi mata allurar rigakafin ciwon Limoniya.
Zai dauki kwanaki kafin a tantance ko Merkel mai shekaru 65 ta harbu da wannan cuta ta murar Coronavirus ko COVID-19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu