Cuba-Corona-Italy

Tawagar Likitocin Cuba sun isa Italiya domin aikin agaji

Likitocin Cuba da suka isa Italia domin taimakawa kasar shawo kan annobar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayuka sun samu kyakyawar tarba, inda aka dinga musu tafi lokacin da suka sauka a jirgi.

Wasu jami'an lafiya yayin aikin bayar da agajin cutar Corona.
Wasu jami'an lafiya yayin aikin bayar da agajin cutar Corona. AFP
Talla

Yankin Lombardy da ke Italia ne ya bukaci taimakon hukumomin Cuban wadanda suka yi suna wajen ba da gudumawar kula da lafiya a kasashe da dama.

Kasar Cuba tun daga shekarar 1959 ke taimakawa kasashen duniya da likitoci, musamman kasashe mataulata wajen shawo kan matsalolin da ke tattare da harkar lafiyar jama’a.

Cikin kasashen da suka ci gajiyar irin wannan taimako sun hada da Haiti wadda ta yi fama da cutar kwalara da Kenya da ke fama da karancin likitoci sai kuma Yankin Afirka ta Yamma da ya yi fama da cutar Ebola.

Wannan ne karo na farko da Cuba ke tura tawaga zuwa Italia, daya daga cikin kasashe masu arziki saboda gamsuwa da rawar da likitocin ta ke takawa.

Jagoran likitocin 52 Leornado Fernandez ya ce dukkan su suna fargabar wannan cuta amma kuma hakkin su ne su taimaka wajen kare lafiyar jama’a.

Ya zuwa yanzu akalla mutane kusan 5,500 suka mutu a kasar sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI