Faransa

Coronavirus ta halaka karin likitoci 4 a Faransa

Gwamnatin Kasar Faransa tace likitoci guda 4 sun kara mutuwa yayinda suke kokarin ceto rayukan mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar.

Wasu likitocin kasar Faransa.
Wasu likitocin kasar Faransa. AFP
Talla

Daya daga cikin likitocin dake Mulhouse kusa da iyakar Switzerland da Jamus, ya kamu da cutar ce daga wani mara lafiyar da yake kula da shi, yayinda Magajin Garin Metz yace wani likitan ya mutu a asibitin Saint-Avoid.

Yanzu haka an samu mutuwar likitoci guda 5 tun bayan barkewar cutar wadda ta kasha mutane sama da 600 a kasar ta Faransa.

Jami’an lafiya sun yi gargadin cewar asibitocin Faransa da dama sun soma yiwa dimbin marasa lafiyar da suka kamu da cutar Coronavirus kadan duk kuwa da kafa asibitocin wucin gadi na sojoji da gwamnati tayi domin maganace matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI