Faransa-Coronavirus

Faransa ta amince da gwajin Chloroquine don magance cutar Corona

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da ministan lafiyar kasar Olivier Véran.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da ministan lafiyar kasar Olivier Véran. Bertrand Guay/Pool via REUTERS

Ministan Lafiyar Faransa Olivier Veran yace kamfanin dake sarrafa Chloroquine ya baiwa kasar umurnin amfani da maganin wajen baiwa mutanen da cutar coronavirus ta yiwa illa amma tilas sai da sa idon likitoci.

Talla

Ministan yace majalisar kula da harkokin lafiya ta amince da shirin amfani da maganin idan bukatar haka tayi ga marasa lafiyar dake cikin hadari idan likitoci sun amince da bukatar yin haka.

Wannan mataki yayi daidai da na shugaban Amurka Donald Trump wanda yace sun dauki matakin gaggawa domin samar da maganin ga Amurkawa.

Shan maganin na Chloroquine don rigakafi ko magance cutar murar Coronavirus ba bisa ka’ida ba, yayi sanadin jikkata mutane a biranen Legas da Abuja a Najeriya kamar yadda rahotanni daga sahihan majiyoyi suka tabbatar.

Wadanda maganin ya zamewa guba dai sun ruga shagunan saida magunguna ne jim kadan bayan sauraron jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a ranar alhamis kan amincewa da soma gwajin Chloroquine din a matsayin maganin cutar Coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.