Ingila

Yarima Charles ya kamu da cutar Coronavirus

Yarima Charles na kasar Birtaniya. 4/3/2020.
Yarima Charles na kasar Birtaniya. 4/3/2020. Victoria Jones/Pool via REUTERS/File Photo

Fadar Sarauniyar Ingila ta sanar da cewar Yarima Charles dake jiran sarautar kasar ya kamu da cutar coronavirus wadda tuni ta hallaka mutane 422 a kasar.

Talla

Sanarwar fadar tace Yariman mai shekaru 71 ya nuna alamun cutar a jiin sa amma kuma yana cikin koshin lafiya a inda ya killace kan sa a Scotland tare da uwargidan sa Camilla wadda aka tabbatar bata dauke da cutar bayan gwajin da aka mata.

Fadar tace mahaifiyar sa Sarauniya Elizabeth ta biyu mai shekaru 93 wadda bata gamu da Yariman ba a cikin makwanni biyu da suka gabata tana cikin koshin lafiya.

Ita dai Sarauniya Elizabeth da mijin ta Yarima Philips mai shekaru 98 sun koma fadar Windsor dake wajen birnin Lagos tun daga ranar 19 ga watan nan.

Mai magana da yawun Sarauniyar tace tun daga ranar 12 ga watan nan, sarauniyar bata hada ido da Yarima Charles ba kuma ta na cigaba da bin shawarwarin da masana kiwon lafiya suka bata.

Tuni Firaminista Boris Johnson ya kafa dokar hana fita da kuma hana mutane sama da biyu taruwa domin hana yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI