Amurka

Amurka ta ware dala tiriliyon 2 don tallafa wa wadanda coronavirus ta shafa

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. AFP Photos/Getty Images North America/Alex Wong

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da shirin tallafin Dala triliyan 2 domin tallafawa Yan kasar dake fama da cutar coronavirus da taimakawa asibitoci da kuma tattalin arzikin kasar dake neman durkushewa.

Talla

Shirin tallafin ya kunshi baiwa Amurkawan dake biyan haraji tallafin kudade a matsayin rance domin ceto sana’oin su da kuma kamfanoni, yayin da za’a kara kudin tallafin da ake baiwa marasa aikin yi da kuma samar da kayan da ake bukata a asibitoci.

Shirin ya samu gagarumar rinjaye a Majalisar, yayin da za’a mikawa Majalisar wakilai domin amincewa da shi.

Bayan an mika wa majalisar wakilai kudirin, ana sa ran amincewa da shi zuwa ranar Juma’ar nan.

Wannan kudiri dai ya kunshi batun tallafi na kudi da ya kai dala dubu 3 da dari 4 da za a yi wa iyalan kasar da wannan iftila’in cutar coronavirus ya shafa.

Kudirin ya kumaa yi tanadin tallafi na dala biliyan dari 5 wanda za a raba a matsayin tallafi da rance ga masu sana’o’i da kamfanoni, da kuma dala biliyan 50 ga kamfanonin sufurin jiragen sama da annobar ta shafi sana’o’insu.

Ya kuma tanadi dala biliyn 100 don taimaka wa asibitoci da sauran wuraren kula da lafiya da kayan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.