Coronavirus ta kashe yarinya mai shekaru 16 a Faransa

Jami'an lafiya a kasar Faransa
Jami'an lafiya a kasar Faransa AFP

Gwamnatin Faransa tace mutane 365 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a cikin sa’oi 24 da suka gabata, cikin su harda yarinya mai shekaru 16 a duniya.

Talla

Babban jami’in kula da lafiyar kasar Jerome Salomon ya sanar da wannan sabon adadi wanda shine mafi girma tun bayan barkewar wannan annoba da ta ratsa kasashen duniya sama da 180.

Wannan adadi ya nuna cewar mutanen da suka mutu a Faransa ya kai 1,696 daga cikin mutane 29,155 da suka kamu da cutar.

Italia ce kasar da aka fi samun wadanda suka mutu a cikin sa’oi 24, inda ta sanar da mutuwar mutane 712 a yau, sai kuma Birtaniya wadda ta bayyana cewar mutane sama da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI