Turai

Coronavirus ta yiwa Turai illa fiye da kowace nahiya

Wasu jami'an lafiya a nahiyar Turai.
Wasu jami'an lafiya a nahiyar Turai. AFP/Josep Lago

Kididdigar da hukumomin lafiya suka fitar a baya bayan nan, ta nuna cewar a halin yanzu annobar coronavirus ta fi addabi Turai fiye da kowace nahiya a sassan duniya.

Talla

Alkalumman sun nuna cewa yanzu haka annobar ta coronavirus ta halaka mutane dubu 20 da 59, gami da kama wasu dubu 337 da 632 a nahiyar Turan.

Cutar kuma tafi barna a kasashen Italiya da Spain inda ta halaka rayuka dubu 9 da 134, da kuma dubu 5 da 690.

A Birtaniya kuwa adadin wadanda annobar murar alakakan ta COVID-19 ta halaka a kasar ya zarta dubu 1, bayanda a ranar asabar kadai cutar ta kashe mutane 260, kwana guda bayanda gwaji ya tabbatar da cewar Fira Ministan kasar Boris Johnson ya kamu da cutar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.