Faransa-Italiya

Macron ya yiwa Italiya tayin bata tallafin yakar Coronavirus

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AFP/Ludovic Marin

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin taimakawa Italiya wajen yakar annobar coronavirus bayan da cutar ta halaka mutane 969 a kasar cikin kwana 1, adadi mafi muni tun bayan bullarta a kasar.

Talla

Shugaba Macron yayi tayin ga Italiya ne, yayin zantawa da wasu jaridun kasar ta Italiya ciki har da La Repubblica.

A kwanakin baya ne dai Faransa da Jamus suka fuskanci caccaka daga ciki da wajensu, saboda kin baiwa Italiya taimakon karin takunkuman rufe fuskoki da sauran kayayyakin bukata domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI