Amurka

Trump ya janye aniyar haramta zirga-zirga a New York saboda coronavirus

Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da shirin killace birnin New York da makotansa, gami da haramta shiga da fita daga cikinsu, saboda annobar coronavirus da ke dada karfi a kasar.

Wasu tsirarun mutane a yankin Times Square, dake birnin New York a Amurka, bayan bullar annobar cutar coronavirus a kasar. 19/3/2020.
Wasu tsirarun mutane a yankin Times Square, dake birnin New York a Amurka, bayan bullar annobar cutar coronavirus a kasar. 19/3/2020. REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Da fari dai shugaba Trump da kansa ya gabatar da kudurin shirin na killace birnin New York inda annobar ta fi kamari a Amurka, to amma shugabanni a matakin gwamnatin yankin suka hau kujerar naki kan bukatar, bisa dalilan cewar, matakin zai sanya karin firgici tsakanin al’ummar birnin na New York.

Yanzu haka dai Amurka ta zarta kowace kasa a duniya adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus, da a yanzu suka zarta dubu 115 a jiya asabar, yayinda kuma annobar ta halaka wasu dubu 1 da 900.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI