Faransa

Macron ya tsawaita dokar zaman gida a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, lokacin da yake sanar da tsawaita dokar zaman gida don dakile yaduwar coronavirus.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, lokacin da yake sanar da tsawaita dokar zaman gida don dakile yaduwar coronavirus. Ludovic Marin/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tsawaita aiki da dokar hana fita a kasar har zuwa ranar 11 ga watan mayu mai zuwa don shawo kan annobar coronavirus wadda ta kashe kusan mutane dubu 15 a kasar.

Talla

Macron wanda ke jawabi ga al’ummar kasar a marecen ranar Litinin, ya ce makarantu da gidajen cin abinci za su gaba da kasancewa a rufe, yayin da iyakokin Faransa za su kasance a rufe illa ga ‘yan asalin kasashen yankin Turai kawai

"Ya ku ‘yan uwana, na fito domin gabatar muku da  jawabi a yammacin yau bayan na tattauna da wadanda ke da ruwa da tsaki, ba wani abu ba ne face don in sanar da ku abubuwan da ke jiran mu a cikin makwanni ko kuma watanni masu zuwa. Lalle muna kyakkyawa fata, amma a halin yanzu dai babu tabbas." Inji shugaba Macron.

Shugaban ya kara da cewa, "A duk inda ka zagaya a cikin Faransa za ka tarar cewa asibitoci sun cika sun batse, aiki ya yi wa ma’aikatan kiwon lafiya yawa, abin da ke nufin cewa ya zama wajibi mu ci gaba da daukar matakai tare da yin kira ga jama’a don mutunta shawarwarin da ake ba su."

"Saboda haka ne muka yanke shawarar ci gaba da aiki da dokar hana fita har zuwa ranar Litinin 11 ga watan Mayu mai zuwa, mun dauki wannan mataki ne domin ta hakan kawai ne za mu iya rage yaduwar wannan cuta da kuma samar wa bangaren kiwon lafiya sassauci." A cewar shugaban na Faransa.

Kasashen duniya da dama sun dauki matakan killace jama'a a gidajensu don hana yaduwar cutar coronavirus wadda ta lakume rayuka fiye da dubu 117.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.