Spain

Kasuwa ta bude wa masu kera akwatin gawa

Yadda ake kera akwatin gawa a kauyen Pinor na Spain
Yadda ake kera akwatin gawa a kauyen Pinor na Spain AFP

Kasuwa ta bude wa masu kera akwatin gawa a wani karamin kauye da ake kira Pinor a yankin arewa maso yammacin Spain, lura da yadda cutar coronavirus ke ci gaba da lakume rayuka babu kakkautawa a kasar.

Talla

An kiyasta cewa, a cikin watanni biyu, mutane dubu 18 da 500 ne suka mutu bayan kamuwa da coronavirus a Spain.

Yanzu haka, masu kera akwatin gawar a kauyen Pinor mai yawan al’umma fiye da dubu 1, sun dukufa dare da rana wajen samar da adadi mai yawa na akwatin saboda yadda ake tsananin bukatar sa a sassan Spain, kamar yadda Magajin Garin na Pinor, Jose Luis Gonzale ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP.

A bangare guda, akwatinan gawar da aka saba shiga da su cikin Spain daga kasar China, an dakatar da jigilarsu, lamarin da ya kara tsananta bukatar su don yi wa daruruwan mamata jana’iza cikin gaggawa.

Masu kera akwatinan a garin na Pinor na fuskantar tarin kalubalen samar da su cikin kankanin lokaci, abin da ya sa suka daina yi wa akwatinan ado don gaggauta samar da  adadi mai yawan gaske.

Kimanin mutane 600 zuwa 700 ko ma fiye da haka na mutuwa a kowacce rana a Spain saboda annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.