Italiya

Likitocin Italiya 150 sun rasa rayukansu yayin yakar coronavirus

Wasu likitocin kasar Italiya a daya daga cikin cibiyoyin kula da mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a birnin Rome.
Wasu likitocin kasar Italiya a daya daga cikin cibiyoyin kula da mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a birnin Rome. Alberto Pizzoli/AFP/Getty Images

Kungiyar likitocin kasar Italiya sun ce mambobin su sama da 150 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, yayinda da suke aikin ceto rayuwar jama’a.

Talla

Kungiyar likitocin tace zuwa ranar 9 ga wannan wata na Afrilu, likitoci 100 suka mutu, amma a halin yanzu adadin ya kai 151.

A jiya kawai mutane 333 suka mutu a Italiya abinda ya kara yawan mutanen da suka mutu sakamakon wannan annoba a kasar zuwa dubu 26 da 977.

Firaminista Giusseppe Conte ya bayyana shirin bude kofofin kasar domin baiwa jama’a damar walwala daga ranar litinin mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI