Faransa-Coronavirus

Jami'an tsaro sun cafke masu fasa kaurin dubban kyallayen rufe fuska

Kamen kyallayen rufe fuskar na bayan fage dubu 140, shi ne mafi girma da 'yan sandan Faransa suka yi a baya bayan nan.
Kamen kyallayen rufe fuskar na bayan fage dubu 140, shi ne mafi girma da 'yan sandan Faransa suka yi a baya bayan nan. FRANCK FIFE AFP/File

Yan Sanda a Faransa sun kama wasu mutane dake dauke da kyallayen rufa baki da hanci dubu 140, da aka boye domin sayar da shi ta bayan fage, a daidai lokacin da mutane ke matukar bukatarsa.

Talla

Yan Sandan sun ce sun kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu wajen boye kyallayen a Saint-Dennis, yayinda daya daga cikinsu ta bayyana cewar ta sayo su ne daga Netherlands akan dala dubu 87.

Gwamnatin Faransa ta haramta sake sayar da kyallen rufe fuska a kasar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake kwace kyallen rufe fuska daga hannun gungun mutanen dake shirin saidawa ta bayan fage a birnin Paris ba, bayan bullar annobar coronavirus a kasar.

A makwannin da suka gabata jami’an tsaron Faransa sun kama wasu mutane dauke da kyallayen rufe fuska dubu 29 a yankin Aubervilliers da zummar sayar da su ta bayan fage, sai kuma wasu kyallayen dubu 32 da aka kama a Saint-Ouen, a arewacin birnin Paris.

Yawan mutanen da cutar coronavirus ta kama a Faransa yanzu haka ya haura dubu 160, yayinda annobar ta kashe wasu kusan dubu 23.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI