Amurka

Coronavirus ta sake halaka Amurkawa sama da dubu 2 a rana 1

Watan ma'aikaciyar lafiya a harabar cibiyar kula da masu cutar coronavirus ta Maimonides Medical Center dake Brooklyn a birnin New York na Amurka. 2/4/2020.
Watan ma'aikaciyar lafiya a harabar cibiyar kula da masu cutar coronavirus ta Maimonides Medical Center dake Brooklyn a birnin New York na Amurka. 2/4/2020. (Spencer Platt/Getty Images/AFP)

Jami’ar Johns Hopkins dake sanya ido kan yadda cutar COVID-19 ke yaduwa a Amurka tace a jiya mutane sama da dubu 2 suka mutu sakamakon wannan annoba.

Talla

Alkaluman da Jami’ar ta bayar sun nuna cewar mutane dubu 2 da 53 suka mutu a jiya sabanin 2,502 da aka samu a ranar laraba, abinda ya kawo adadin wadanda cutar ta kasha a Amurka zuwa 62,906.

Kwanaki 2 da suka gabata ne dai jami’ar ta Johns Hopkins dake Amurka tace annobar ta coronavirus ta halaka mutane dubu 2 da 502 a fadin kasar a cikin sa’oi 24 a tsakanin ranakun talata da kuma larabar da suka gabata, wato 28 da kuma 29 ga watan Afrilu.

Annobar coronavirus dai na cigaba da yiwa Amurka ta’adi fiye da kowace kasa a duniya, inda a yanzu haka ta halaka jimillar mutane dubu 61 da 717.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.