Amurka

COVID-19 ta raba Amurkawa sama da miliyan 30 da ayyukansu

Wasu Amurkawa cikin layi a birnin New York City. 1/4/2020.
Wasu Amurkawa cikin layi a birnin New York City. 1/4/2020. Stephanie Keith/Getty Images

Adadin Amurkawan da suka rasa ayyukanyi ya zarce miliyan 30, sakamakon yadda annobar coronavirus ke cigaba da yin tasiri wajen durkusar da tattalin arzikin kasashen duniya ciki harda na Amurka.

Talla

Tarihi ya nuna cewar jimillar wadanda suka rasa ayyukan nasu a Amurkan shi ne adadi mafi yawa da kasar ta taba gani tun shekarar 1930.

Alkaluman da gwamnatin Amurka ta fitar cikin daren jiya Alhamis ya nuna mutane miliyan 30 da dubu dari 3 ne suka cike takaddun neman tallafin rage radadi sakamakon yadda suka rasa ayyukansu, adadin da ke nuna a jumlace Amurkawa miliyan 30 da dubu dari 8 ne yanzu haka ke zauna babu aikinyi, cikin abin da bai wuce makwanni 6 da matakin kulle kasuwanci don dakile yaduwar corona ba.

Tuni dai al'ummar kasar suka fara matsa kaimi ga gwamnati don ganin an sassauta dokar ci gaba da killace jama'a a gida ta hanyar bayar da damar bude wasu sassa na kasuwanci a kasar ta Amurka.

Masu hasashe dai na ganin yawan marasa aikin yin ka iya zarce kashi 20 a Amurkan, dai dai lokacin da wani rahoto na daban ke nuna duk mutum ko kamfani 1 cikin 6 ya tagayyara daga cutar ta coronavirus adadin da ke matsayin kwatankwacin al'ummar jihar Texas.

A bangare guda itama tarayyar Turai wadda ke fuskantar koma bayan tattalin arziki mafi muni a tarihi bayan hadakar 1995, hasashen ya nuna tattalin arzikin Faransa zai ruguzo da kashi 5.8 wanda ke matsayin mafi muni da kasar ta gani bayan 1949, yayinda tattalin arzikin Spain zai sauka da kashi 5.2 yayinda Jamus za ta fuskanci mafi munin koma baya a tattalin arziki da kashi 6.3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.