Faransa-Coronavirus

Faransa ta tsawaita dokar ta bacin yakar annobar COVID-19 da watanni 2

Yadda kasuwanni a Faransa suka kasasance a rufe, saboda dokar hana zirga-zirgar dake aiki don yakar annobar coronavirus.
Yadda kasuwanni a Faransa suka kasasance a rufe, saboda dokar hana zirga-zirgar dake aiki don yakar annobar coronavirus. AFP

Gwamnatin Faransa ta tsawaita dokar ta bacin da ta kafa a kasar domin yaki da annobar COVID-19 har zuwa ranar 24 ga watan Yuli dake tafe.

Talla

Ministan lafiyar kasar Olivier Veran yace ranar litinin mai zuwa za’a kai kudirin dokar Majalisar dokoki domin amincewa da karin watannin biyu da akayi domin hana cutar sake dawowa.

Dokar ta kunshi bada damar killace duk bakin dake shiga kasar saboda abinda ministan cikin gida Christophe Casterner yace zasu cigaba da zama da cutar na dogon lokaci.

Mai Magana da yawun gwamnatin Sibeth Ndiaye tace a ranar litinin za’a gabatarwa Majalisar dokoki da kuma ta wakilai kudirorin domin amincewa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.