Rasha

Coronavirus ta kama 'yan Rasha kusan dubu 10 cikin kwana 1

Wasu likitoci a Moscow, babban birnin kasar Rasha yayin daukar maras lafiyar da ya kamu da cutar COVID-19.   Moscow on Wednesday. (AP)
Wasu likitoci a Moscow, babban birnin kasar Rasha yayin daukar maras lafiyar da ya kamu da cutar COVID-19. Moscow on Wednesday. (AP) AP

Hukumomin Rasha sun ce mutane kusan dubu 10 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar cikin kwana guda.

Talla

Alkalumman ma’aikatar lafiyar kasar na baya bayan nan ya nuna cewar, jumillar yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai dubu 123 da 54, bayan karin mutane dubu 9 da 623 da annobar ta kama cikin sa’o’i 24.

Bayanai sun ce a birnin Moscow kadai karin mutane dubu 5 da 358 suka kamu da cutar a kwana 1, jumillarsu kuma dubu 62, 658, a babban birnin kasar at Rasha.

Tuni dai Fira Ministan Rasha Mikhail Mishustin ya shiga cikin jerin fitattun mutanen duniya da suka kamu da cutar coronavirus.

Yanzu haka dai annobar ta halaka mutane dubu 1 da 222 tun bayan bulla a kasar ta Rasha.

Magajin garin birnin Moscow dake Rasha, Sergei Sobyanin yace kashi biyu na mazauna birinin ko kuma mutane sama da dubu 250 sun harbu da cutar coronavirus.

A sakon da ya aike Magajin Garin yace gwajin da aka yiwa jama’a ne ya nuna wannan adadi mai tayar da hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.