Yawan Faransawan da COVID-19 ke halakawa duk rana ya ragu
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Faransa tace mutane mutane 135 annobar COVID-19 ta halaka mata cikin sa’o’I 24 da suka shude, adadi mamata mafi karanci da kasar ta gani cikin makwanni 6, tun bayan ranar 22 ga watan Maris kenan.
Adadin nay au lahadi ya karawa hukumomin kasar kwarin gwiwar cewa, kaifin annobar ya ragu matuka, la’akari da cewa, a jiya asabar mutane 166 cutar ta halaka a kasar.
Yanzu haka dai wanna annoba ta halaka jumillar Faransawa dubu 25 da 827.
Daga ranar 11 ga watan Mayun nan ne kuma gwamnatin Faransar za ta sassauta dokar hana fitar da ta kafa a daukacin kasar tun ranar 17 ga watan Maris, domin dakile annobar coronavirus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu