Amurka

Corona za ta rika kashe Amurkawa dubu 3 kullum a watan Mayu - Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Reuters

Gwamnatin Amurka tayi hasashen cewar akalla Amurkawa 3,000 zasu mutu kowacce rana daga wannan wata na Mayu, yayin da mutane 200,000 zasu kamu da cutar coronavirus kowace rana.

Talla

Wani rahoton asiri na gwamnati da jaridun New York Times da Washington Post suka wallafa, ya kwatanta rahotan da kuma adadin da ake samu yanzu na mutane 25,000 zuwa 30,000 dake kamuwa da cutar da kuma mutane 1,500 zuwa 2,000 dake mutuwa kowacce rana.

Fadar shugaban Amurka dai bata ce uffan ba dangane da rahotan ba, wanda yayi karo da matsayin shugaba Donald Trump cewar baya tunanin wadanda zasu mutu sakamakon annobar COVID-19 a kasar zasu wuce 100,000.

Hasashen mutuwar karin dubban Amurkawan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Donald Trump ya kafe kan tuhumar China da cewar, da gangan ta kirkiri cutar coronavirus da ta addabi duniya a daya daga cikin cibiyoyin gwaje-gwajenta dake birnin Wuhan.

Trump na cigaba da nanata tuhumar Chinan ce, duk da cewa kwarru dake gamayyar kungiyoyin leken asirin Amurka sun ce bincikensu ya tabbatar da cewa, coronavirus Ikon Allah ce, ba wai dan adam bane ya kirkireta ko kuma ya sauya mata halitta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.