Rasha

Coronavirus ta sake kama karin 'yan Rasha sama da dubu 10 a rana 1

Likitoci a wata cibiyar kula da masu cutar coronavirus a Moscow, babban birnin kasar Rasha.
Likitoci a wata cibiyar kula da masu cutar coronavirus a Moscow, babban birnin kasar Rasha. Sofya Sandurskaya/Moscow News Agency/Handout via REUTERS

Rasha ta tabbatar da samun sabbin mutane dubu 10 da 633 da suka kamu da cutar coronavirus a cikin sa’oi 24, adadi mafi girma da kasar ta samu a rana guda.

Talla

Wannan ya sa adadin mutanen da suka kamu da cutar ya tashi zuwa dubu 134 da 686, abinda ya kai kasar mataki na 7 a jerin kasashen duniya dake fama da annobar ta COVID-19.

Adadin wadanda suka mutu a kasar kuma ya tashi zuwa 1,280 bayan samun mutane 58 da suka kamu da cutar.

A ranar 2 ga watan Maris hukumomin kasar ta Rasha suka bayyana cewar ‘yan kasar akalla dubu 9 da 623 annobar ta kama cikin sa’o’i 24.

Bayanai sun ce a birnin Moscow kadai karin mutane dubu 5 da 358 suka kamu da cutar a kwana 1, jumillarsu kuma dubu 62, 658, a babban birnin kasar at Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.