Coronavirus

Birtaniya ta koma kasa ta 2 a duniya da coronavirus ta fi yiwa barna

Mutane sanye da takunkuman rufe baki da hanci a kasuwar Broadway dake birnin London, a Birtaniya. 3/5/2020.
Mutane sanye da takunkuman rufe baki da hanci a kasuwar Broadway dake birnin London, a Birtaniya. 3/5/2020. REUTERS/Henry Nicholls

Birtaniya ta zama kasa ta biyu da annobar coronavirus ko COVID-19 ta fi yi ta’adi, bayanda ta halaka sama da mutane dubu 32,000, adadin da ya sa ta komawa kan matsayi na 2 duniya bayan Amurka.

Talla

A yanzu haka Birtaniya ce kasa ta farko a Turai kuma ta biyu a duniya mafi asarar rayukan da corona ta lakume mata, a yayin da Amurka ke matsayi na farko da adadin mutum dubu 68 da 700 wadanda corona ta kashe.

Sabon yanayin da Birtaniya ta tsinci kanta a ciki na zuwa ne daidai lokacin da Rasha ke samun karuwar dubban mutanen da suke kamuwa da cutar, inda a yanzu take da jumillar mutum dubu 155 masu dauke da ita.

Yanzu haka dai kasuwannin hada-hada a Turai da Amurka sun fara dawowa hayyacinsu inda ake fatan daidaituwar farashin man fetur a kasuwannin duniya sakamakon sassauta matakan hana yaduwar cutar da kasashe suka dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.