Amurka

Coronavirus ta halaka Amurkawa dubu 2,333 cikin sa'o'i 24

Jami'an lafiyar Amurka a Brooklyn dake birnin New York, yayin daukar gawarwakin wadanda annobar coronavirus ta halaka.
Jami'an lafiyar Amurka a Brooklyn dake birnin New York, yayin daukar gawarwakin wadanda annobar coronavirus ta halaka. REUTERS/Andrew Kelly

Jami’ar Johns Hopkins dake Amurka, tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a fadin kasar a cikin sa’oi 24, sun kai 2,333, abinda ya ribanya adadin da aka samu a ranar Talata.

Talla

A ranar litinin da ta gabata kasar ta samu adadi mafi karanci na mutane dubu 1 da 15 da suka mutu a wannan wata, kafin adadin yayi tashin gauran zabi a jiya.

Ya zuwa yanzu mutane dubu 71 da 22 suka mutu, a Amurka, tun bayan barkewar annobar a kasar, yayin da shugaba Donald Trump ke cigaba da bayyana matsayin sa na ganin an koma gudanar da harkokin yau da kullum a kasar.

A farkon makon nan, Gwamnatin Amurka tayi hasashen cewar akalla Amurkawa 3,000 zasu mutu kowacce rana daga wannan wata na Mayu, yayin da mutane 200,000 zasu kamu da cutar coronavirus kowace rana.

Fadar shugaban Amurka dai bata ce uffan ba dangane da rahotan ba, wanda yayi karo da matsayin shugaba Donald Trump cewar baya tunanin wadanda zasu mutu sakamakon annobar COVID-19 a kasar zasu wuce 100,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.